Wednesday, August 26, 2020

FAฦŠAKARWA GARE MU A YAU, #RanarHausa2020

 


Daga Dr. Abubakar Kusfa


Ba sabon abu ba ne, kuma ba a ษ“oye ya ke ba, yadda rayuwar Malam Bahaushe ya ke a sarฦ™e da addini. Ka iya cewa, yadda addini ya shiga cikin al'adun Hausa, tamkar yadda hazo ke shigewa cikin juna ne, su cuษ—e, su zama girgije bai ษ—aya.


Toh amma ba fa dukkan al'adun na bahaushe ne suke daidai da addini ba. Idan na ce Addini, ina nufin Musulunci. Domin kuwa, shi Addinin ba na Hausawa kaษ—ai ba ne. Hasali ma, ya sauka ne da yaran Larabawa, tare da cewa kuma ba addinin larabawan ba ne, addini ne na ษ—aukacin duniya.


Idan muka yi la'akari da dambarwar duniyar mu a yau, mu Hausawa da yadda al'amuran mu suka rincaษ“e, muka ษ—auki tafarkin ruษ—u da ruษ—ewa, za mu ga cewa ummul aba'isan hakan shi ne watsi da mu ka yi da al'adunmu waษ—anda basu ci karo da addini ba. Musulunci bai hana al'ada ba,


idan har bata ci karo da koyarwar addini ba. Misali mu ษ—auki yawan auri-saki da ya addabe mu cikin ฦดan lokutan nan da muke ciki. ฦ˜ididdiga da ban san asalin ta ba, tace kusan kashi sittin na auratayya yanzu ba su wuce shekara sai ka ji an rabu. An ce kunne ya girmi kaka, haka ne?


Masu shekaru a cikin mu, manyan mu irin su Farfesa Dr. Usman Modibo, Farfesa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, da waษ—ansu da yawa, cikin waษ—anda su ne tabarau na hangen nesa da muke da shi, kuma zakarun gwajin dafi da suke raye a cikin mu a yau, tabbas su na da abun faษ—i idan suka yi la'akari da jiya,


suka kwatanta jiyar da yau. Yadda muke sanya tufafin mu, mazanmu da matan mu, yadda muke ฦ™ara hazaฦ™a wajen karatun Mahammadiyya da na boko, yadda muke ashararanci da rashin girmama manya, su kuma manyan da yin halin ko ina kula da ฦ™anana, da dai sauran taษ“ara sun girmama!


Yanzu haka za mu cigaba? Yanzu haka za mu bar al'amuran mu su sake lalacewa? Yanzu haka za mu zura ido mu rayu babu shugabanci ฦ™waฦ™ฦ™wara a arewa? Shin kuwa hakan zai haifa mana ษ—a mai ido? 


Al'umma na iya rayuwa babu shugabanci? Ba bu mai kwaษ“a ma wani? Anya? #RanarHausa2020


Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya. Amma ya zama wajibi, tilas, mu zauna mu yi wa juna karatun ta natsu. Mu bar ฦ™yashi da ji-ji da kai. Mu bar wa juna haddasa. Mu guji taษ—iye wa juna ฦ™afafu. Mu haษ—a ฦ™arfi da ฦ™arfe mu cicciษ“i arewa mu kai ta tudun mun tsira.


#alhudahuda247

Sunday, August 23, 2020

A Safiyar Yau Lahadi Rikici Ya Barke Tsakanin Jami'an Tsaro Da 'Yan Kugiyar IPOB 'Yan Kabilar Igbo A Emene, Ta Enugu

An bayar da rahoton cewa mutane da yawa sun mutu lokacin da wasu mambobin kungiyar IPOB 'yan kabilar Igbo suka yi artabu da 'yan sanda a jihar Enugu ranar Lahadi.

‘Yan sanda sun mamaye wani gini lokacin da mambobin kungiyar IPOB suke wani taro a Emene a Enugu. An bayar da rahoton yin artabu da 'yan kugiyar, lamarin da ya sa 'yan sanda su yi amfani da karfi.

Wannan ya haifar da rikici tsakanin ‘yan kungiyar IPOB da jami’an‘ yan sanda da suka fara harbin da bindiga. An ce nan da nan aka tura wata tawaga daga jami’an tsaro zuwa wurin da abin ya faru sannan kuma suka sami damar kama da yawa daga cikin ‘yan kungiyar IPOB. 

Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, amma wani ganau ya ce “mutane da dama” sun rasa rayukansu a rikicin.

Daniel Ndukwe, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, ba a iya samun damar yin magana dashi ba har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton. 

Tashin hankalin na ranar Lahadi shine na baya-bayan nan a tsakanin 'yan sanda da membobin kungiyar IPOB tun lokacin da gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta'adda.

Daruruwan masu fafutukar kafa kasar Biafran da aka kama yayin gangaminsu da makamantan su, a sassa daban-daban na kudu maso gabas yanzu haka suna fuskantar shari'a.

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...