Babban bankin Najeriya wato CBN ta magantu game da bayyanan da ake ta yaษata game da cire rubutun larabci (Ajami), da ku buga takardar ฦudi na Naira ₦2,000 Da ₦5,000
A ci gaba da shirin sake fasalin wasu takardun ฦudi, wasu ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun yi ta rade-radin cewa babban bankin zai buga takardar ฦudi ta Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000).
Babban bankin Najeriya, CBN, ta musanta wani shiri da ake yi na buga takardun ฦudi na Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000) a ฦasar.
Sai dai Daraktan Ayyuka na ฦudi na CBN, Ahmed Bello-Umar, yayin wata tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka a ranar Litinin, ya jaddada cewa har yanzu babbar takardar ฦudin a Najeriya shine Naira dubu ษaya ₦1,000.
Yayin da yake kira ga ฦดan Najeriya da su yi hattara da ฦดan damfara da dillalan labaran karya, Mista Umar ya ce duk wanda aka kama da takardun ฦudi na bogi ya kamata a kai rahoto ga jami’an tsaro.
Ya kara da cewa babu kamshin gaskiya game da buga takardar ฦudi da sama da Naira dubu ษaya (₦1,000), don haka, babu wani abu kamar ₦2,000, ₦5,000, ko kuma ₦ 10,000 kamar yadda ake yadawa.
Mafi girman darajar Naira har yanzu ₦1000 ne. Kuma a yanzu, babu wani dalili ko shirin ฦarawa.
Ya kamata mutane su yi taka tsantsan don kada ฦดan damfara su ruษe su. A gaskiya, idan wani ya zo maka da irin wannan kudin na jabu, muna ba mutane shawara su kai rahoto ga hukumomin tsaro.
Da yake magana kan cece-kucen da ake yi kan rubutun Larabci (Ajami) a kan ฦudin Naira, Mista Umar ya yi kira ga ฦดan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa hukumar CBN ba za ta dauki duk wani mataki da zai yi watsi da bukatun jama’a ba.
Muna sane da cewa wasu sun garzaya kotu; wasu na cewa a cire shi, wani bangaren kuma na cewa kada a cire shi. Amma ina so in yi kira ga kowa da kowa ya nutsu.
Hukumomin CBN da ma shugaban ฦasa ba za su dauki matakin da zai haifar da tarzoma tsakanin al’umma ba. Ya kamata kowa ya nutsu, babu wannan magana ta cire rubutun larabci (Ajami) a jikin ฦudadan da za'a sabunta, in ji shi.
Dangane da matakin wayar da kan jama’a game da sake fasalin kudin Naira, musamman a yankunan karkara, Mista Umar ya ce CBN za ta gudanar da wani gagarumin gangamin wayar da kan jama’a da zarar shugaban ฦasa ya kaddamar da sabbin takardun ฦudi na Naira.
Al-Hudahuda 24/7: Muryar Talaka/Kafar Al'umma
No comments:
Post a Comment