Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦan Bindiga A Walmart Na ฦasar Amurka
ฦณan sanda sun ce wani ษan bindiga ya harbe mutane da dama a wani shagon Walmart da yammacin jiya Talata a jihar Virginia ta Amurka, ya kuma kara da cewa wanda ake zargi da harbin bindiga guda daya ya mutu.
Harin ฦดan bindiga a birnin Chesapeake na zuwa ne a daidai lokacin da Amurkawa ke gudanar da bikin godiya (thanks giving), kuma ya biyo bayan wani harin da aka kai a wani mashaya na ฦดan luwadi da madigo da ke jihar Colorado da yammacin Asabar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar.
Babban mai sayar da kayayyaki a Amurka, a Walmart, ya fitar da wata sanarwa da sanyin safiyar Laraba yana mai cewa: "Mun yi matukar kaduwa da wannan mummunan lamari."
Rahotanni sun ce akalla mutane 10 ne aka sanar da sun mutu a harin.
Ku biyo mu domin samun labarai da bidiyoyi masu ฦayatarwa