Mulkin Kasar Afghanistan dai a yau ya koma hannun Taliban, sai naga ya dace na warware wasu daya cikin alโummar mu wani abu mai rikitarwa game da su:
(1) Wannn suna Taliban, a harcen su na Pashtun yana nufin jamโin dalibai, kamar Musulman ne, abinda ke nufi jamโin Musulmi, su Dalibai ne wadanda suka gogu a karatun zaure, kamar yadda yake a alโadar Kasar su
(2) Mazhabarsu ta Aqeedah Maturidiyya ce ta Abu Mansur Almaturidi, daya ne daga cikin manyan Malaman Sunnah na zamaninsa, Mazhabarsa tana kusa sosai da Mazhabar Abul Hasanil Ashโari.
Yadda wasu suke munana zato a garesu, Taliban a gurin โyan Boko Haram da ISIS suna musu kallon โyan bidiโah ne wadanda jininsu ya halatta, saboda wai Taliban sun sabawa mazhabar Salafiyya wadanda suke binta
(3) Taliban Mazhabarsu ta Fiqhu Hanafiyya suke bi, don Mazahabarsa ce ta yadu a Kasashen su tun farkon zuwan Musulunci, kuma da ita suke shariโah, kamar dai mu nan Nigeria muke bin mazhabar Malikiyyah
(4) Taliban basu da dangantaka da wata kungiyar taโaddancin addini ko siyasa, balle kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi
(5) Amurka ta tuhumi Taliban da goyon bayan taโaddanci saboda kin mika musu Usama bin Laden don su hukuntashi a shekarar 2001, su kuwa Taliban sunyi aiki da ilmin da suka sani wanda ya haramta sallama Musulmi ga kafurai, har suka yarda da gushewar mulkinsu akan dabbaka Sunnar Manzon Allah (SAW)
(6) Taliban kwararru ne kuma gogaggu ne a iya mulkin jamaโa, ba kamar yadda kafofin yada labaran turai ke bata su ba, ko da yake baโa rasa su da wata kura-kurai wadanda ba wani โdan adam dake iya rabuwa da kuskure, amma alherinsu yafi kuskurensu yawa nesa ba kusa ba.
Kuma mulkinsu a Kasar Afghanistan yafi na Amurkawa masu yada addinin Kiristanci karfi da yaki, kamar yadda yafi na Iran da take kokarin shiga ta yayyaga Kasar, ta yada shiโanci kamar yadda takeyi yanzu haka a Iraqi
(7) Wasu mutane na yi musu hukunci da nauโin tufafinsu, ace wai suna tauye hakkin mata, suna yi musu kulle, wannan ba haka bane, irin tufafinsu na alโada suke sawa mazansu da matansu, ko zaman Amurka a Kasar na shekara 20 bai canza matansu daga yin lullubi da sanya niqabi ba
(8) Bayyanar kungiyoyi masu daโawar jihadi na duniya irinsu Boko Haram, ISIS da sauransu ya sa wasu Musulmi ba su son jin maganar jihadi, abinda ke sa su jin tsoron Taliban, alhali Taliban ta banbanta da irin wadancan kungiyoyi masu yawan kafirta Musulmi.
Su Taliban mutane ne masu kokarin adalci hatta ga abokan gabar su, kuma kasancewar su jagorori a Kasar Afghanistan yafi alheri akan Amurka (Kafirai) ko Iran โyan shiโah
Allah Ka daukaka Musulunci da Musulmai a duk inda suke Amin