Saturday, August 21, 2021

Matasa Sun Kona Masallaci Kurms


A Jahar Delta Dake Kudu Maso Kudancin Najeriya.


Matasan "Jeddo" da ke Karamar Hukumar Okpe a Jihar Delta sun bi Musulmai masu ibada da kuma Hausa tare da kona wani masallaci kurmus, da sunan yin zanga-zangan nuna rashin amincewarsu da kisan shugaban ’yan banga na yankin, mai suna George Akiru wanda aka fi sani da Scosco wanda ba  asan ko suwaye suka kashe shi ba.

Matasan sun zargi Hausawa da cewa sune suka shirya wannan aika-aika ba tare da hujja ba na zargin Hausawa da aikata laifin.

Kisan shugaban 'yan banga ya haifar da tashin hankali a yankin yayin da matasan suka sha alwashin daukar fansar mutuwar mamacin.

Wani matashi a cikin unguwar, Ubada Umukoro, wanda ya zanta da manema labarai ya ce, "Ba da jimawa ba za mu sake kai hari saboda sun kashe dan asalin garin nan."

Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe, a tattaunawar wayar tarho da DAILY POST, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don bankado wadanda suka kashe shugaban‘ yan banga.

No comments:

Post a Comment

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...