Kungiyar IPOB masu fafutukar kafa kasar Biafra 'yan kabilar Igbo sun kai hare-hare kan Hausawa mazauna karamar hukumar Oyigbo ta jihar Ribas a ranar Asabar 5 ga Satumba da Lahadi 6 ga Satumba, inda aka kashe Hausawa biyu.
Wasu mutane biyu sun samu munanan rauni na harbin bindiga a harin kuma sunyi barazanar kai hare-hare kan al’ummar Hausawa.
Wani shaidar gani da ido ya ce: “lamarin, wanda yake kama da hada baki ne aka fara ranar Asabar har zuwa Lahadi. Wasu matasa 'yan kungiyar IPOB sun mamaye yankin da galibi' Hausawa ne suna zaune tare da kai musu hari da muggan makamai. Mutum biyu sun mutu a harin yayin da wasu mutum biyu suka samu munanan raunuka,”.
Kakakin kungiyar 'yan Arewa mazauna jihar Ribas, Alhaji Musa Saidu ya yi tir da Allah wadai da harin yayin da yake tabbatar da mummunan harin.
Musa ya ce: lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan kungiyar IPOB da ke dauke da muggan makamai suka kai hari a wani yanki da ke Oyigbo wanda ke da yawan Hausawa.
Ya ce harin wanda ya faru a ranakun Asabar da Lahadi ya yi sanadiyar mutuwan Hausawa biyu 'yan kasuwa yayin da mutum biyu suka ji munanan raunuka.
Ya ce ba zai iya tantance dalilin da ya sa aka kai harin ba amma ya nuna cewa harin na iya zama wani bangare ne na barazanar da ‘yan kungiyar IPOB suka yi wa al’ummar Hausawa a Jihar Ribas a baya.
Shugaban karamar hukumar Oyigbo, Prince Gerald Oforji ya yi tir da harin tare da yin kira ga Hausawa mazauna Oyigbo da su kwantar da hankulansu kada su dauki doka a hannunsu.
#alhudahuda247
No comments:
Post a Comment