Barka Da Shigowa Shafin 𝐀𝐥-𝐇𝐮𝐝𝐚𝐡𝐮𝐝𝐚 𝟐𝟒/𝟕: Kafa Ce Da Take Gudanar Da Aiyukanta A Yanar Gizo-Gizo, Dake Kawo Ingantatun Labarai Kamar Yadda Suke, A Lokacin Da Manyan Kafofin Yada Labarai, Suke Kokarin Sakayesu, Da Kuma Fadakarwa, Tunatarwa A Wasu Lokutanma Harda Ilimantarwa. Allah Ya Taimake Mu Damu Da Ku, Ya Kuma Bamu Sa'a
Saturday, November 12, 2022
GASKIYAN AL'AMARI GAME DA HOTUNAN WASU LALATATUN KUƊAƊEN DA AKE TA YAƊAWA A KAFOFIN SADA ZUMUNTA
Wednesday, November 9, 2022
ƊAN TAKARAR JAM'IYYAR PDP YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA A JAHAR BORNO
Tuesday, November 8, 2022
DA ƊUMI-ƊUMI: WATA KOTU A NAJERIYA TA BUƘACI A TASA ƘEYAR SHUGABAN HUKUMAR EFCC ZUWA GIDAN GYARAN HALI
Monday, November 7, 2022
Zaben 2023: Siyasar Ƙabilanci Har Tasa...
CBN Ta Ce Cire Rubutun Larabci Da Buga ₦2,000 Da ₦5,000
Babban bankin Najeriya wato CBN ta magantu game da bayyanan da ake ta yaɗata game da cire rubutun larabci (Ajami), da ku buga takardar ƙudi na Naira ₦2,000 Da ₦5,000
A ci gaba da shirin sake fasalin wasu takardun ƙudi, wasu ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun yi ta rade-radin cewa babban bankin zai buga takardar ƙudi ta Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000).
Babban bankin Najeriya, CBN, ta musanta wani shiri da ake yi na buga takardun ƙudi na Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000) a ƙasar.
Sai dai Daraktan Ayyuka na ƙudi na CBN, Ahmed Bello-Umar, yayin wata tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka a ranar Litinin, ya jaddada cewa har yanzu babbar takardar ƙudin a Najeriya shine Naira dubu ɗaya ₦1,000.
Yayin da yake kira ga ƴan Najeriya da su yi hattara da ƴan damfara da dillalan labaran karya, Mista Umar ya ce duk wanda aka kama da takardun ƙudi na bogi ya kamata a kai rahoto ga jami’an tsaro.
Ya kara da cewa babu kamshin gaskiya game da buga takardar ƙudi da sama da Naira dubu ɗaya (₦1,000), don haka, babu wani abu kamar ₦2,000, ₦5,000, ko kuma ₦ 10,000 kamar yadda ake yadawa.
Mafi girman darajar Naira har yanzu ₦1000 ne. Kuma a yanzu, babu wani dalili ko shirin ƙarawa.
Ya kamata mutane su yi taka tsantsan don kada ƴan damfara su ruɗe su. A gaskiya, idan wani ya zo maka da irin wannan kudin na jabu, muna ba mutane shawara su kai rahoto ga hukumomin tsaro.
Da yake magana kan cece-kucen da ake yi kan rubutun Larabci (Ajami) a kan ƙudin Naira, Mista Umar ya yi kira ga ƴan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa hukumar CBN ba za ta dauki duk wani mataki da zai yi watsi da bukatun jama’a ba.
Muna sane da cewa wasu sun garzaya kotu; wasu na cewa a cire shi, wani bangaren kuma na cewa kada a cire shi. Amma ina so in yi kira ga kowa da kowa ya nutsu.
Hukumomin CBN da ma shugaban ƙasa ba za su dauki matakin da zai haifar da tarzoma tsakanin al’umma ba. Ya kamata kowa ya nutsu, babu wannan magana ta cire rubutun larabci (Ajami) a jikin ƙudadan da za'a sabunta, in ji shi.
Dangane da matakin wayar da kan jama’a game da sake fasalin kudin Naira, musamman a yankunan karkara, Mista Umar ya ce CBN za ta gudanar da wani gagarumin gangamin wayar da kan jama’a da zarar shugaban ƙasa ya kaddamar da sabbin takardun ƙudi na Naira.
Al-Hudahuda 24/7: Muryar Talaka/Kafar Al'umma
Sunday, November 6, 2022
Zaku Iya Sauraran Sunnah Radio Kai Tsaye
Harin Ƴan Bindiga Na Ƙara Ta'azzara A Ƙasar Amurka
Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin Ɗan Bindiga A Walmart Na Ƙasar Amurka Ƴan sanda sun ce wani ɗan bindiga ya harbe mutane da da...

-
Daga Zahraddeen Gandu Mawakin Siyasar Nan Dauda Kahutu Ra-Ra-Ra Ya Kusan Shan duka A Wajen Shooting Din Sabuwar Wakarsa Mai Suna 'JIHA...
-
The Killings between Jukum and Tivs only get brush by the Media. You hardly hear Ortom or Darius name in some Media But Kaduna; AIT, Channe...
-
We want to draw the attention of the Kaduna state government and general public about the ongoing gorilla attacks and murder of Muslim Fula...