A yau idan kace zakayi aure, daga ranar da ka fara fafu-tuka, zuwa ranar auren ka, in bakai wasa ba sai wando ya daina zama a Qugun ka saboda tsadar aure, tun daga sadaki, kayan lefe da kudin gaisuwar uwa da uba da sauran su.
Wannan yasa samari da dama suka gazayin aure.
Amma yau idan kayi niyyar yin zini a rana daya indai kana iyawa zaka iyayi da mata 20 ko sama da haka, kuma kudin da zaka kashe bazai kai dubu hamsin ba, wasuma ko sisi basa kashewa, kyauta sukeyi.
Sabida yam matanan gasunan kamar jamfa a Jos, kuma suna bukatar auren amma samari ba kudi, iyaye kuma kudin sukeso.
Wannan yasa aka taru aka hada karfi da karfe tsakanin samari da yam mata aketa sabawa Allah kullum.
Zina kuwa na daya daga cikin manyan laifuka masu kawo fitintinu a wanga duniyar tamu.
Na daga cikin kawo karshen Zinace-zinace, shine farashin aure ya fado kasa warwas!, domin babban abun bukata a aure shine sadaki, shima idan babu ana badawa bashi, duk fa musulunci yayi hakane domin a rage fasadi a doron kasa.
Amma niko Malam banko tabaji da ganin anyi aure bashi ba.
Hasali ma, Idan wannan shekaran farashin sadaki na dubu hamsinne, to tabbata shekara mai zuwa a dubu tamanin zaka ji shi.
Sai dai nasan farashin sadaki yana yin tsadane bisa dalilin talauci da ake fama dashi, domin ko nawa iyayen yarinya suka amsa a matsayin sadaki basu ke cinyewa a cikin su ba, karawa kudin yawa suke domin suyiwa yar tasu kayan daki dan a fita kunya, nasan da wannan...
Ita kuma kunya anaso a fice tane a gurin yan gutsiri tsoma, wadanda idan ba'ayiwa yarinya kayan a zo a gani ba zasubi unguwa suna gulmace-gulmace, karshe ya koma gori wajen Amarya... Wannan yasa iyaye ke tsauwala kudin sadaki.
To amma, sai suka manta cewa ita kunya ta Uban-giji ake gudu, ba ta wani masabi ba...
Domin idan diyarka tayi cikin shege a gidanka sai kafi kowa jin kunya a duniya, kuma wannan shine abin kunya da ake gudu, amma ba kunyar kayan lefe ko sadaki ba, sabida haka a daina gudun maganganun wannan
Wannan haka yake nikaina Ina bukatan aure amma gaskiya da anyimin maganan aure sau gabana yafadi Ba komai nake tsoroba illa tsadar auren
ReplyDeleteAllah dai yasa mudace