Daga Dr. Abubakar Kusfa
Ba sabon abu ba ne, kuma ba a ɓoye ya ke ba, yadda rayuwar Malam Bahaushe ya ke a sarƙe da addini. Ka iya cewa, yadda addini ya shiga cikin al'adun Hausa, tamkar yadda hazo ke shigewa cikin juna ne, su cuɗe, su zama girgije bai ɗaya.
Toh amma ba fa dukkan al'adun na bahaushe ne suke daidai da addini ba. Idan na ce Addini, ina nufin Musulunci. Domin kuwa, shi Addinin ba na Hausawa kaɗai ba ne. Hasali ma, ya sauka ne da yaran Larabawa, tare da cewa kuma ba addinin larabawan ba ne, addini ne na ɗaukacin duniya.
Idan muka yi la'akari da dambarwar duniyar mu a yau, mu Hausawa da yadda al'amuran mu suka rincaɓe, muka ɗauki tafarkin ruɗu da ruɗewa, za mu ga cewa ummul aba'isan hakan shi ne watsi da mu ka yi da al'adunmu waɗanda basu ci karo da addini ba. Musulunci bai hana al'ada ba,
idan har bata ci karo da koyarwar addini ba. Misali mu ɗauki yawan auri-saki da ya addabe mu cikin ƴan lokutan nan da muke ciki. Ƙididdiga da ban san asalin ta ba, tace kusan kashi sittin na auratayya yanzu ba su wuce shekara sai ka ji an rabu. An ce kunne ya girmi kaka, haka ne?
Masu shekaru a cikin mu, manyan mu irin su Farfesa Dr. Usman Modibo, Farfesa Dr. Hakeem Baba-Ahmed, da waɗansu da yawa, cikin waɗanda su ne tabarau na hangen nesa da muke da shi, kuma zakarun gwajin dafi da suke raye a cikin mu a yau, tabbas su na da abun faɗi idan suka yi la'akari da jiya,
suka kwatanta jiyar da yau. Yadda muke sanya tufafin mu, mazanmu da matan mu, yadda muke ƙara hazaƙa wajen karatun Mahammadiyya da na boko, yadda muke ashararanci da rashin girmama manya, su kuma manyan da yin halin ko ina kula da ƙanana, da dai sauran taɓara sun girmama!
Yanzu haka za mu cigaba? Yanzu haka za mu bar al'amuran mu su sake lalacewa? Yanzu haka za mu zura ido mu rayu babu shugabanci ƙwaƙƙwara a arewa? Shin kuwa hakan zai haifa mana ɗa mai ido?
Al'umma na iya rayuwa babu shugabanci? Ba bu mai kwaɓa ma wani? Anya? #RanarHausa2020
Dabara dai ta rage ga mai shiga rijiya. Amma ya zama wajibi, tilas, mu zauna mu yi wa juna karatun ta natsu. Mu bar ƙyashi da ji-ji da kai. Mu bar wa juna haddasa. Mu guji taɗiye wa juna ƙafafu. Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu cicciɓi arewa mu kai ta tudun mun tsira.
#alhudahuda247

No comments:
Post a Comment