Wednesday, August 19, 2020

GAREKU MATASA MUSAMMAN MASU SHA'AWAR HARKOKIN SIYASA.

 

Daga Dan'uwanku Matashi Abdullahi Hassan

.

.


Kira na gareku yan'uwa matasa yakamata hankulan mu sudawo jikin mu, Mu farka mu san mike mana ciwo muna son rayuwar mu tayi inganci muma wata rana iyayene kuma mune zamu jagoranci alummah.


Inhar muka fahimci hakan to lallai fada da juna banamu bane inbamu shawara kar mu yarda mu biyema yan siyasa suna hadamu fada da juna saboda biyan bukatar kansu hatta kai muna jin zafi hassada gaba da juna sukuma suna chan suna jin dadin rayuwarsu suda iyalansu, Shawara ta garemu kar ka yadda don uwanka matashi kuna jamiyya daya yabarta kudawo kuna cin zarafi junanku, Ko Kuna gidan dan siyasa yabar gidan kudawo kuna cin mutuncin junanku wanda shi yasaka ko bashi yasaka ba hakan illa ce garemu matasa.


Kuma yau Allah na iya ba wanda kake gaba ko fada da danuwanka matashi nasara ya banzatar dakai baima son ganinka ko jin sunanka balle ka amfana dashi ga shinan muna gani misalai sunfi shurin masaki agaban mu na irin haka wanine chan baisan hawa ba baisan sabka ba zaizo ya amfana kaikuma ya watsar dakai. 


Danuwanka matashi yau Allah na iya bashi dama ya taimakeka kokai Allah yabaka damar ka taimakeshi, Inhar ko muka tsaya bisa wannan mumunar alqiblar babu ranar da zamuga cigaba wadancan din dai sune da yayansu zasu cigaba mulkarmu da azabtar damu saboda babu da akida tunani da manufa atare damu.


Yakamata hankulan mu sudawo jikin mu, Mugane kanmu muke tarwatsawa da yakar junan mu wallahi kada mubiyema wadannan da wannan kazamar siyasar ta cigaba da tarwatsawa mana rayuwa.


In kunne yaji........

1 comment:

  1. LALLAI MUTANEN AREWA SUNA CIKIN DAMUWA TA CIWON HASSADA GA JUNANMU

    ReplyDelete

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...