Tuesday, August 18, 2020

Dalilin Dake Dakushe Mutanan Arewa Daga Samu Taimakon Rance Ko Tallafin Gwamnati

 

Daga Al-Ameen Batsari


Rashin Register Kasuwanci na daya daga abubuwan da suke dakushe mutanen Arewa daga samun taimakon rance ko tallafin Gwamnati.


Sai kaga mutum na da shago 10 wuri daban daban shi kadai, amma bai da ko takardar burodi dake nuna shi Dan kasuwa ne. Ko kuma kaga mutum ya shekara 10 yana Sana'a, ya kware amma bai da takardar dake nuna ya Iya Sana'ar nan.


Ita kuma Gwamnati a tsarin ta, tana bukatar shaida don tabbatar da kana kasuwanci ko sana'a. In rance za a bada ko tallafi, wanda zayyi approving din rancen ko tallafin yana Lagos ko Abuja, bai san ka ba, bai taba kila zuwa garin da kake ba. Saboda haka takarda kadai zai gani ya gamsu ka Iya Sana'ar ko kana kasuwancin.


Na biyu ita Gwamnati duk abinda zata yi tana yi ne don habaka tattalin arziki. Shi kuma habaka tattalin arziki jigo shine karuwar haraji. Saboda haka, duk wanda za a ba tallafi, so ake yi ya habaka, ya dauki wasu aiki, ya kuma rika biyan haraji. Idan yana haka, zai gamsar da Gwamnati abu 2:.

I) Ka Zama employer of labour

II) Ka na bada Gudummuwa wajen habakar tattalin arziki da haraji.


Don haka, takarda nada muhimmanci. Mu canza salon kasuwanci da Sana'a na gargajiya, zuwa salon kasuwanci na zamani.


Allah ya taimaka



No comments:

Post a Comment

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...