Saturday, November 12, 2022

GASKIYAN AL'AMARI GAME DA HOTUNAN WASU LALATATUN KUฦŠAฦŠEN DA AKE TA YAฦŠAWA A KAFOFIN SADA ZUMUNTA

Hotunan matattun kudin da ake yaษ—awa a kafofin sada zumunta, da sunan wai wasu ne suka boye har suka lalace ba gaskiya bane.

Kuษ—aษ—e ne wanda suka lalace wanda ake kira da (mutilated money) a turance, irin wanda ya yi dameji bankuna suke mayarwa babban bankin Najeriya, wato CBN, hotunan su ฦดan barandan gwamnati suke daukowa suna yadawa domin kokarin kare manufar gwamnati akan ฦ™udirinta na chanja fasalin wasu daga cikin kuษ—aษ—en ฦ™asar

Babu ฦ™amshin gaskiya game da hotunan da aka yaษ—awa wai wasu ne suka boye kuษ—aษ—en har suka lalace.

Al-Hudahuda 24/7: Muryar Talaka/Kafar Al'umma

Wednesday, November 9, 2022

ฦŠAN TAKARAR JAM'IYYAR PDP YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA A JAHAR BORNO

Yadda ษ—an takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP ya tsallake rijiya da baya a Maiduguri babban birnin jahar Borno

Wasu mahara wanda ake kyautata zaton ฦดan bagan siyasa ne, suka farmaki tawagar, Atiku Abubakar, ษ—an takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP,  a Maiduguri babban birnin jahar Borno, a ranr laraba, a lokacin da yaje yaฦ™in neman zabe a jahar...


...An kai harin ne a lokacin da motocin ke kan hanya zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke tsakiyar birnin na Maiduguri, domin yi wa magoya bayansa jawabi.

A harin an raunata sama da mutane dari da hamsin 150, kawo yanzu dai babu wani ฦ™arin haske da mahukunta ko kuma hukumar tsaro ta jahar ta fitar game da lamarin.





Tuesday, November 8, 2022

Monday, November 7, 2022

Zaben 2023: Siyasar ฦ˜abilanci Har Tasa...

Gwamnan Benue ya fadi wasu maganganu na rashin hankali da kuma borin kunya a gaban takwarorinsa, ganin ya rasa madafa a siyasar 2023 shi da abokan hauragiyarsa.

Gwamnan jahar Benin da siyasar ฦ™abilanci,
jiya lahadi gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya karbi bakwancin wasu Gwamnonin kudร ncin Nigeria karkashin jagorancin Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike

A cikin jawabin da Samuel Ortom yayi, yace sakamakon harin da fulani makiyaya suke yiwa jama'arsa a Benue to ba zai taba goyon bayan takaran duk wani jinsin fulani ba, watakila zai goyi bayan Tinubu...


...Har yace ya gwammace ya mutu akan ya goyi bayan takaran Atiku bafulatani, wai ba zai taba zama bawan fulani ba, wato saboda wannan Gwamnan ya rasa alkibla da madogara sai ya dauki matsalar tsaron jiharsa ya jibgata akan kabilanci

To wannan babbar nasarace ga siyasar Atiku, dama na jima ina jin tsoro ace a cikin tawagar Atiku akwai miy@gun mutane masu haddasa rikicjn kabilanci a Nigeria irin Gwamna Samuel Ortom

Domin idan jama'a basu manta ba Samuel Ortom shine Gwamna na farko da ya kawo tsarin koran fulani makiyaya daga jihar Benue saboda tsanar da ya yiwa Hausa/Fulani, yana daukar wannan matakin sai ya bude kofar barna, aka wayi gari Gwamnonin yankin Inyamurai da na Yarbawa suka kwaikwayeshi

Lissafin siyasar Atiku yana cigaba da tafiya daidai, makiyin da zai boye kiyayya ya yake ka, yafi illa akan makiyin da ya bayyana kiyayyarsa da wuri

Sannan jama'ar Arewacin Nigeria wannan ya sa ku kara fahimtar nagartan Atiku, su wadannan Gwamnonin suna son su tankwara Atiku ne, ya musu yadda suke so, shi kuma ya tsaya akan ra'ayinsa, Atiku ba zai taba zama shugaban da za'a juyashi ba Insha Allah

Atiku ne gatan mu jama'ar Arewacin Nigeria, shine yake kishin mu da gaske, Atiku namu ne, shiyasa makiyan mu suka fara yakarsa tun daga yanzu saboda sun hango masa nasara, don haka ku zo mu hadu mu bashi dukkan gudunmawa da goyon baya

Idan juninsu kabilanci ai babu kabilar da ta kai Hausa/Fulani yawa a Nigeria, don haka siyasar 2023 siyasace ta kabilanci, zamuyi nasara akan su Insha Allah
 
#Alhudahuda247
#MuryarTalaka
#KafarAlumma
Datti Assalafiy ✍️

CBN Ta Ce Cire Rubutun Larabci Da Buga ₦2,000 Da ₦5,000


 Babban bankin Najeriya wato CBN ta magantu game da bayyanan da ake ta yaษ—ata game da cire rubutun larabci (Ajami), da ku buga takardar ฦ™udi na Naira ₦2,000 Da ₦5,000

A ci gaba da shirin sake fasalin wasu takardun ฦ™udi, wasu ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta sun yi ta rade-radin cewa babban bankin zai buga takardar ฦ™udi ta Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000).

Babban bankin Najeriya, CBN, ta musanta wani shiri da ake yi na buga takardun ฦ™udi na Naira dubu biyu (₦2,000) da kuma Naira dubu biyar (₦5,000) a ฦ™asar.  

Sai dai Daraktan Ayyuka na ฦ™udi na CBN, Ahmed Bello-Umar, yayin wata tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka a ranar Litinin, ya jaddada cewa har yanzu babbar takardar ฦ™udin a Najeriya shine Naira dubu ษ—aya ₦1,000. 

Yayin da yake kira ga ฦดan Najeriya da su yi hattara da ฦดan damfara da dillalan labaran karya, Mista Umar ya ce duk wanda aka kama da takardun ฦ™udi na bogi ya kamata a kai rahoto ga jami’an tsaro. 

Ya kara da cewa babu kamshin gaskiya game da buga takardar ฦ™udi da sama da Naira dubu ษ—aya (₦1,000), don haka, babu wani abu kamar ₦2,000, ₦5,000, ko kuma ₦ 10,000 kamar yadda ake yadawa.

Mafi girman darajar Naira har yanzu ₦1000 ne. Kuma a yanzu, babu wani dalili ko shirin ฦ™arawa.

Ya kamata mutane su yi taka tsantsan don kada ฦดan damfara su ruษ—e su. A gaskiya, idan wani ya zo maka da irin wannan kudin na jabu, muna ba mutane shawara su kai rahoto ga hukumomin tsaro. 

Da yake magana kan cece-kucen da ake yi kan rubutun Larabci (Ajami) a kan ฦ™udin Naira, Mista Umar ya yi kira ga ฦดan Najeriya da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa hukumar CBN ba za ta dauki duk wani mataki da zai yi watsi da bukatun jama’a ba. 

Muna sane da cewa wasu sun garzaya kotu; wasu na cewa a cire shi, wani bangaren kuma na cewa kada a cire shi. Amma ina so in yi kira ga kowa da kowa ya nutsu.

Hukumomin CBN da ma shugaban ฦ™asa ba za su dauki matakin da zai haifar da tarzoma tsakanin al’umma ba. Ya kamata kowa ya nutsu, babu wannan magana ta cire rubutun larabci (Ajami) a jikin ฦ™udadan da za'a sabunta, in ji shi. 

Dangane da matakin wayar da kan jama’a game da sake fasalin kudin Naira, musamman a yankunan karkara, Mista Umar ya ce CBN za ta gudanar da wani gagarumin gangamin wayar da kan jama’a da zarar shugaban ฦ™asa ya kaddamar da sabbin takardun ฦ™udi na Naira.

Al-Hudahuda 24/7: Muryar Talaka/Kafar Al'umma

Sunday, November 6, 2022

Zaku Iya Sauraran Sunnah Radio Kai Tsaye

Sunnah Radio Akan Manhajar Ta AA๐Ÿ‘‡https://appho.st/d/txom3f8h

Shin Kana Da Wayar Android? Kuma Kana Buqatar Dukkan Karatukan Maluman Sunnah?

Wannan Application An Yi Shine Domin Saukaka Muku Wurin Samun Dukkan Karatukan Maluman Sunnah Cikin Sauqi.

Ku Sauke Shi A Wayar Ku, Ku Fada Mana Yadda Kuka Yi Amfani Da Shi.

Domin Saukewa Taba Link Dake Kasa
๐Ÿ‘‡

AA Sabon Dandalin Sada Zumunta

Monday, August 22, 2022

Kira Zuwa Ga Gwamnati Da Jam'iyyan Tsoran Najeriya...

Game Da Kisan Gillar Da Akayiwa Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashu'a (Rahimahullah)...

Kira Zuwa Ga Gwamnatin Nijeriya, Karkashin Shugabancin, Shugaba Muhammadu Buhari, Da Rundunar Sojojin Najeriya, HQ Nigerian Army  Karkashin Jagorancin, Manjo Janar Farouk Yahya, Da Dukkan Masu Ruwa Da Tsaki Akan Harkar Tsaron ฦ˜asar Nan...

...Game Da Kisan Gillar Da Wasu Wulakantatun Sojojin Najeriya, "Lance Corporal Adamu Gideon" Da "Lance Corporal John Gabriel" Wanda Suke Aiki Karkashin Bataliya Ta 241, Nguru, Jahar Yobe, A Najeriya, Suka Yiwa Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashu'a (Rahimahullah). Kamar Yadda Hukumar 'Yan Sandan Najeriya Reshan Jahar Yobe Ta Tabbar.

Daga Al-Asad Al-Amin ✍️
                   • Al-Asad Al-Amin

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ฦ˜ai.

Ina Fatan Allah Yasa Wannan Sakon Zata Kai Inda Muke Son Takai, Kuma Muna Fatan Wannan Sakon Zai Kai Ga Hukumar Tsoran ฦ˜asar Nan Zasu Karanta Wannan Sakon Da Idon Basira.

A Matsayinmu Na Musulmai, 'Yan Najeriya, Masu Ko Karin Bin Doka Da Odar ฦ˜asar Nan, Wanda Aka Yima 'Dan Uwanmu Kisan Gillar, Muna Jan Hakalin Gwamnatin ฦ˜asar Nan Da Hukumar Tsoran ฦ˜asar Nan, Da Cewa, Kisan Babban Shehin Malamin Addinin Musulunci, Kamar Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashu'a, Kuma Gwamnati Ta Yi Shuru Gami Da Nuna Halin Ko In Kula Game Da Lamarin, Babban Barazanace Ga Tsoran ฦ˜asar Nan Da Kuma Zaman Lafiya ฦ˜asar.

Duk Da Munji Cewa Rundunar Sojojin Najeriya Reshan Jahar Yobe, Sunyi Ikiranin Gudanar Da Bincike Game Da Alamarin, Toh, A Matsayinmu Na 'Yan Uwansa Musulmai, 'Yan Najeriya, Muna Buqatar Da A Bayyarwa Duniya Sakamakon Bincike Gamida Gaggauta Huntasu Makisan, Domin Ya Zama Izina Ga Sojoji Masu Irin Wannan Mummunar Tunanin, Yin Hakan Shine Zaman Lafiya ฦ˜asar Nan.

A Matsayinmu Ma Musulmai 'Yan Najeriya, Wanda Muke Kokarin Bin Doka Da Odar Wanda Kasar, Wanda Bamu Yarda Da Daukar Doka A Hannu Bah, Daukar Dokar Da Ya Dace Ga Hukumomi, Shine Kadai Zai Iya Kawar Da Akuwar Hakan.

Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashu'a (Rahimahullah), Malamine Mutumin Kirki 'Dan ฦ˜asa Na Gari, Wanda Dubun Dubatan Jama'a Suke Karuwa Da Shi, Wanda Kirkinsa Ne Ya Kai Shi Ga Aukawa Ga Wannan Lamarin, Dole Ne A Hukunta Wadanda Suka Kashe Shi, A Kuma Wayyana Wa Duniya, Kamar Yadda Aka Nuna Wa Duniya Game Da Makishin Hanifa, Domin Mu San Irin Hukuncin Da Aka Yi Musu. 

Bazamu Nade Hannu Mu Zuba Ido, Batare Da An Hukunta Makisan, Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashu'a (Rahimahullah), Ba.

Allah Ya Karbi Shahadar  ๐Ÿคฒ Amin Ya Huyyu Ya Qayyum ๐Ÿคฒ

Mutaimaka Mu Yada Wannan Sakon Domin Sakon Ya Kai Inda Ya Dace.๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...