Wednesday, July 29, 2020

Shawara Zuwaga Masatan Arewa

Aminci a gare ku ya ku matasan yankin Arewa!

A matsayina na daya daga cikinku zanyi amfani da wannan dama na tunatar damu wasu muhimman abubuwa da suke hakki ne a gare mu amma muke yin sakaci da su.

Sanin kowa ne cewa matasa sune kashin bayan kowace al'umma, domin kuwa sune iyaye kuma shugabannin gobe.

Haka ne ma yasa masana masu hangen nesa suka ce duk al'ummar da matasanta suka hada kansu suka zama tsintsiya mai madauri 'daya, to wannan al'umma nan gaba za ta zama ja gaba a kowane irin fanni na rayuwa, ta kuma yi wa sauran al'ummomin zamanin fin-cin-kau.

Shi kuma hadin kannan ba zai samu a tsakaninmu ba har sai mun yarda mun kuma dauki Arewa a dunkule ma'ana, mu gamsu cewa da Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, da duk wani yanki na Arewa, Arewa ce, duk abin da ya samu wani sashe na Arewa walau farin ciki ko akasinsa, mu daukwa cewa Arewa ya shafa gaba 'daya.

Mu kuma gamsu da cewar za mu tallafawa junanmu, kuma za mu mutunta junanmu domin samun nasarar abin da muka sanya a gaba. Ko shakka babu, idan muka samu wannan, to mun kama hanyar tunkara tare da samun mafita kan dumbin matsalolin da suka yi mana daurin gwarmai.

Matasan Arewa bai kamata mu koma gefe muna ganin laifin shugabanni, sarakuna, malamai da manyan Arewa kadai ba, duk wani abu na rashin dadi daya faru sai mu dora musu laifi muna fadin ba sa kishin Arewa. 

Zahirin gaskiya wannan ba daidai bane, kuma ban yarda wadannan jagororin Arewa sune ke da laifi kadai ba, idan har suna da laifi to muma muna da namu laifin. 

Saboda kuwa idan manya sun kasa mai zai sa mu kuma muyi shiru mu kasa cewa komai?

Misali a matsayinmu na shugabannin gobe wane irin shiri mukayi don daukar wannan nauyi? 

Shin mun san tun lokacin da Sardauna, Tafawa Balewa da Aminu Kano suka fara gwagwarmaya? 

Idan muka koma tarihi zamu ga sun fara gwagwarmaya akan Arewa tun suna da karancin shekarun da basu fi 20 zuwa 30 ba. 

To mu fa yaushe zamu fara? 

A matsayinmu na masu ikirarin kishin na Arewa.

Shin tawa ne hali zamu kawowa kanmu mafita?

Amma saboda saukin wannan tambaya zanyi kirinkin bada amsarta. 

Amsar tambayar itace mu matasa mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinmu daya, bayan haka kuma mu zama masu kishi da soyayyar yankinmu. 

A karshe nayi amfani da wannan dama ne don na isar da wannan sako ga duk wani matashi wannan sakon, saboda sanin wannan ce hanya kadai da zan aika sakon nawa kuma ya isa zuwa wurin wadanda na aika dominsu. 

Fatan duk wanda ya karanta wannan sakon zai aikawa sauran abokansa ta haka ne zata samu isa zuwa ga duk wani matashi mai kishin Arewa.

A ฦ™arshe Inna rokon Allah Ya ษ—aukaki wannan yanki namu Na Arewa da ฦ™asarmu Najeriya.

Ya kawo mana zaman lafiya mai ษ—orewa, Ya ba mu shugabanni nagari.

Inna roฦ™on Allah Ya sa wannan sakon ya kai ga waษ—anda nayi dominsu Ya kuma ba su ikon aikawa sauran abokansu.

No comments:

Post a Comment

Harin ฦณan Bindiga Na ฦ˜ara Ta'azzara A ฦ˜asar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin ฦŠan Bindiga A Walmart Na ฦ˜asar Amurka ฦณan sanda sun ce wani ษ—an bindiga ya harbe mutane da da...