Wednesday, November 23, 2022

Harin Ƴan Bindiga Na Ƙara Ta'azzara A Ƙasar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin Ɗan Bindiga A Walmart Na Ƙasar Amurka
Ƴan sanda sun ce wani ɗan bindiga ya harbe mutane da dama a wani shagon Walmart da yammacin jiya Talata a jihar Virginia ta Amurka, ya kuma kara da cewa wanda ake zargi da harbin bindiga guda daya ya mutu. 

Harin ƴan bindiga a birnin Chesapeake na zuwa ne a daidai lokacin da Amurkawa ke gudanar da bikin godiya (thanks giving), kuma ya biyo bayan wani harin da aka kai a wani mashaya na ƴan luwadi da madigo da ke jihar Colorado da yammacin Asabar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane biyar. 
Babban mai sayar da kayayyaki a Amurka, a Walmart, ya fitar da wata sanarwa da sanyin safiyar Laraba yana mai cewa: "Mun yi matukar kaduwa da wannan mummunan lamari." 

Rahotanni sun ce akalla mutane 10 ne aka sanar da sun mutu a harin. 

Ku biyo mu domin samun labarai da bidiyoyi masu ƙayatarwa

Wednesday, November 16, 2022

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Yana Cikin Tsaka Mai Wuya

Sun Fara Barazanar Zasu Chanja Sheƙa Daga Tafiyar Jam'iyyar APC.

Zaɓen 2023: Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC Yana Cikin Tsaka Mai Wuya

Ƴan Social Media Din Arewa Da Wasu Ƙungiyoyin Da Suke Tallata Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sun Yi Barazanar Daina Tallarsa Sakamakon Jam'iyyar Da Kuma Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Ɗan Takarar Basa Yi Dasu, Kuma Babu Su A Cikin Tsarin Yaƙin Neman Zaɓen.

Wasu Daga Cikin Suma Har Sun Fara Barazanar Zasu Chanja Sheƙa Daga Tafiyar Jam'iyyar.


Tuesday, November 15, 2022

ZAMU SANAR DA DUNIYA HALIN DA JAM'IYYAR MU TA APC KE CIKI MADAMAR HAKAN YA CIGABA DA FARUWA - Cewar Ƙungiyoyin Da Ke Goyan Bayan Tinubu

Kada su bari muje kafafen watsa labarai da jaridu domin gaya wa duniya abin da muke ta fama da shi a jam’iyyarmu ta APC. 

Jan Hankali Ne Daga Duk Kungiyoyin Da Suke Goyan Bayan APC Da Dan Takarar Mu Sanata Bola Ahmed Tuníbu.

Kira ga shugabanmu, Sanata Bola Ahmed Tinubu da majalisar yakin neman zaben shugaban ƙasa (PCC) da su duba akwai take-take da wasu jiga-jigan APC masu faɗa a ji na jam'iyyar suke yi, na kai in ba wani bane baza a yi da kai ba sun yi amfani da tsarin wazan ƙaddamar da yaƙin neman zaben shugaban ƙasa a jahar Filato, domin duk ƙungiyoyin da suke goyon bayan ɗan takarar jam'iyar mu ta APC babu wani bayani ga kungiyoyin jam'iyyar mu ta APC, domin taro jahar Filato a hukumance. 

 Tambayar anan shine shin tsarin nasu da ake kira, zai iya tafiyar da dukkan tsarin yakin neman zabe ta fuskar hada kan jama'a? 

Idan aka yi la'akari da batutuwan a nan, da alama fashewar za ta yi tsanani sosai idan ba a aiwatar da ƙungiyoyin tallafi ba. Ba za mu yarda mu maimaita iri abun da ya faru da mu a baya ba, kuma muna tsammanin sakamako daban-daban. 

Mun yi irin wannan a 2015, 2019 kuma yanzu 2023 yana nan, aiki tuƙuru na babu lada da kuɗaɗen albarkatu ga ƙungiyoyin domin gudanar da aikin Kàmfen. 

Me ke faruwa da APC da gaske? Ƙungiyoyin sama da 4,500 waɗanda aka tattance su, menene yanzu manufar irin waɗannan ayyukan an matsa musu gaba ɗaya? 

Wani yanayi mai ban tsoro da kungiyoyin ke samun kansu a Filato a yanzu. An ƙi duk kiran da aka yi. Wane hali ne? Bari a san cewa, rarrabuwar kawuna na tushen tallafi na iya haifar da tsagewa mai tsanani tare da barazana ga nasararmu. 

Ba za ku iya ƙware mu don sake amfani da mu irin na 2015-2019 ba, don yin aiki ga jam'iyya, kuma har yanzu ba a bamu komai ba. APC wace hanya ce gaba? Me ya sa son kai daga shugabanninmu yayi yawa?

 Haka muka yi wa Shugaba Buhari a 2015, da 2019, ba mu samu komai ba, inda Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Buhari/Osinbajo na wancan lokacin ya watsar da kokarinmu ya jefar da mu kamar buhun wake. 

Kada su bar mu je jarida mu gaya wa duniya abin da muke ta fama da shi a jam’iyyarmu. Muna kira ga shugabanni da su ga wannan muguntar da suke tafkawa akan kungiyoyi. 

~Abdullahi Ibrahim Usman 

Saturday, November 12, 2022

GASKIYAN AL'AMARI GAME DA HOTUNAN WASU LALATATUN KUƊAƊEN DA AKE TA YAƊAWA A KAFOFIN SADA ZUMUNTA

Hotunan matattun kudin da ake yaɗawa a kafofin sada zumunta, da sunan wai wasu ne suka boye har suka lalace ba gaskiya bane.

Kuɗaɗe ne wanda suka lalace wanda ake kira da (mutilated money) a turance, irin wanda ya yi dameji bankuna suke mayarwa babban bankin Najeriya, wato CBN, hotunan su ƴan barandan gwamnati suke daukowa suna yadawa domin kokarin kare manufar gwamnati akan ƙudirinta na chanja fasalin wasu daga cikin kuɗaɗen ƙasar

Babu ƙamshin gaskiya game da hotunan da aka yaɗawa wai wasu ne suka boye kuɗaɗen har suka lalace.

Al-Hudahuda 24/7: Muryar Talaka/Kafar Al'umma

Wednesday, November 9, 2022

ƊAN TAKARAR JAM'IYYAR PDP YA TSALLAKE RIJIYA DA BAYA A JAHAR BORNO

Yadda ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar PDP ya tsallake rijiya da baya a Maiduguri babban birnin jahar Borno

Wasu mahara wanda ake kyautata zaton ƴan bagan siyasa ne, suka farmaki tawagar, Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP,  a Maiduguri babban birnin jahar Borno, a ranr laraba, a lokacin da yaje yaƙin neman zabe a jahar...


...An kai harin ne a lokacin da motocin ke kan hanya zuwa dandalin taro na Ramat Square da ke tsakiyar birnin na Maiduguri, domin yi wa magoya bayansa jawabi.

A harin an raunata sama da mutane dari da hamsin 150, kawo yanzu dai babu wani ƙarin haske da mahukunta ko kuma hukumar tsaro ta jahar ta fitar game da lamarin.





Tuesday, November 8, 2022

DA ƊUMI-ƊUMI: WATA KOTU A NAJERIYA TA BUƘACI A TASA ƘEYAR SHUGABAN HUKUMAR EFCC ZUWA GIDAN GYARAN HALI

An kama shugaban hukumar EFCC, AbdulRasheed Bawa, da laifin kin mayar wa wani tsohon Soja motar Range Rover da kudi milyan 40 duk da kotu tayi umurnin mayar masa...


...Hakan tasa kotu ta bada umurci ga Sifeto Janar na ƴan sanda najeriya da ya tasa keyar shugaban hukumar zuwa gidan gyaran hali wato kurkuku 


Monday, November 7, 2022

Zaben 2023: Siyasar Ƙabilanci Har Tasa...

Gwamnan Benue ya fadi wasu maganganu na rashin hankali da kuma borin kunya a gaban takwarorinsa, ganin ya rasa madafa a siyasar 2023 shi da abokan hauragiyarsa.

Gwamnan jahar Benin da siyasar ƙabilanci,
jiya lahadi gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya karbi bakwancin wasu Gwamnonin kudàncin Nigeria karkashin jagorancin Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike

A cikin jawabin da Samuel Ortom yayi, yace sakamakon harin da fulani makiyaya suke yiwa jama'arsa a Benue to ba zai taba goyon bayan takaran duk wani jinsin fulani ba, watakila zai goyi bayan Tinubu...


...Har yace ya gwammace ya mutu akan ya goyi bayan takaran Atiku bafulatani, wai ba zai taba zama bawan fulani ba, wato saboda wannan Gwamnan ya rasa alkibla da madogara sai ya dauki matsalar tsaron jiharsa ya jibgata akan kabilanci

To wannan babbar nasarace ga siyasar Atiku, dama na jima ina jin tsoro ace a cikin tawagar Atiku akwai miy@gun mutane masu haddasa rikicjn kabilanci a Nigeria irin Gwamna Samuel Ortom

Domin idan jama'a basu manta ba Samuel Ortom shine Gwamna na farko da ya kawo tsarin koran fulani makiyaya daga jihar Benue saboda tsanar da ya yiwa Hausa/Fulani, yana daukar wannan matakin sai ya bude kofar barna, aka wayi gari Gwamnonin yankin Inyamurai da na Yarbawa suka kwaikwayeshi

Lissafin siyasar Atiku yana cigaba da tafiya daidai, makiyin da zai boye kiyayya ya yake ka, yafi illa akan makiyin da ya bayyana kiyayyarsa da wuri

Sannan jama'ar Arewacin Nigeria wannan ya sa ku kara fahimtar nagartan Atiku, su wadannan Gwamnonin suna son su tankwara Atiku ne, ya musu yadda suke so, shi kuma ya tsaya akan ra'ayinsa, Atiku ba zai taba zama shugaban da za'a juyashi ba Insha Allah

Atiku ne gatan mu jama'ar Arewacin Nigeria, shine yake kishin mu da gaske, Atiku namu ne, shiyasa makiyan mu suka fara yakarsa tun daga yanzu saboda sun hango masa nasara, don haka ku zo mu hadu mu bashi dukkan gudunmawa da goyon baya

Idan juninsu kabilanci ai babu kabilar da ta kai Hausa/Fulani yawa a Nigeria, don haka siyasar 2023 siyasace ta kabilanci, zamuyi nasara akan su Insha Allah
 
#Alhudahuda247
#MuryarTalaka
#KafarAlumma
Datti Assalafiy ✍️

Harin Ƴan Bindiga Na Ƙara Ta'azzara A Ƙasar Amurka

Mutane 10 Sun Mutu Sakamakon Harin Ɗan Bindiga A Walmart Na Ƙasar Amurka Ƴan sanda sun ce wani ɗan bindiga ya harbe mutane da da...